![]() | |
---|---|
organisms known by a particular common name (en) ![]() | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na |
livestock (en) ![]() |
This taxon is source of (en) ![]() | fata |
Shanu, namiji:Sa, tamace: Saniya, ƙarami:ɗan maraƙi, babba:Bijimi, kalman shanu kuma shine gama-garin jinsi, dabbace mai Ƙafafuwa guda huɗu 4, mutane suna amfani da dabban domin ayyukan gona, kamar huɗa, bajiya, da kuma daukan kaya, kuma suna samun nama, taki, madara da kuma magani daga jikin dabban. Shanu dabbace wacce mahauta suke yawan safaranta saboda tana daga cikin dabbobi da akafi yawan cin namanta a duniya, akan sarrafa naman ta wajen girke girke daban daban, naman shanu tana daga cikin nama masu daɗi da kuma gina jiki.[1][2] Akan sarrafa nonon da ake tatsa ajikin shanun ta hanyoyi daban daban kamar su yogot da sauran su, sannan akan sha nonon shanun da fura ko kuma danbu, akan sha wasu magunguna na gargajiya da nonon shanun.
Ana yin kiwon saniya a gida ana iya yin sa a cikin daji,ako ina ana iya kiwon saniya indai gurin ya kasance ya na da koriyar ciyawa ko busassa
Dabbace wacce ake tatsan madara a hantsan ta.
Ana amfani da shanu a gonaki domin yin huɗa.
Ana amfani da shanu wajen yin wasannin gargajiya, kaman hawan kaho, tsere da dai sauransu.