Kankana | |
---|---|
dan-ice, abinci da melon (en) | |
Tarihi | |
Mai tsarawa | Citrullus lanatus var. lanatus (en) da Citrullus lanatus (en) |
Kankana tana daga cikin Tsirrai waɗanda galibin su shuka su akeyi a gonaki musamman farkon Damina da kuma ƙarshen ta. Ana kiranta da fulatanci da (Pariije) A takaice dai Kankana tsiro ce da ake nomawa don amfani da ita kama daga ganyen ta har zuwa ƴaƴanta. Ko kuma Kankana wata abu ce dake ɗauke da wasu ruwa masu zaƙin gaske waɗanda suke da matuƙar amfani ga jikin Ɗan adam. Kankana tana da amfani sosai a jikin bil'adama Ɗan'adam wayanda bazasu lissafu ba daga cikin su akwai ƙarawa mutum ruwan jiki, kariya daga ciwon daji (cancer), kariya daga ciwon zuciya, da kuma kuzari da dai sauransu.[1] Haka kuma ƴaƴan Kankana suma suna matuƙar amfani don ko ba'a barsu a baya ba wajen gina ko amfani a jikin bil'adama. Misali suna ƙara kuzari ga maza, suna kuma maganin ciwon suga (diabetes) da dai sauransu.[2] Haka kuma Kankana tanada amfani sosai a wajen mata masu juna biyu (masu ciki).[3] Kankana Kuma tana ƙara gyara fata da sanya fata gautsi da sheƙi.[4] Kankana tana kuma maganin ciwon ƙoda da kuma ƙara lafiyar idanu (ido).[5] Amfanin Kankana sunada yawa basu lissafuwa, saboda haka take da muhimmanci a rayuwar mu ta yau da kullum.[6][7][8]
.
Kankana na ɗaya daga cikin kayan gona na marmari da ke da matuƙar amfani ga bil'adama. Kankana wata aba ce mai dauke da ruwa mai zaƙi kuma mai amfani matuƙa ga jikin bil'adama. Masana sun bayyana Kankana da ƴa'ƴan ta mai matuƙar amfani ga rayuwar bil'adama, don sindarai da ke cikinta na Vitamins, Minerals, Antioxidants, da kuma Calories. Wasu daga cikin alfanun Kankana goma sha biyu su ne: