Hukumar Finafinai ta Kenya | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | government agency (en) da film organization (en) |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 2005 |
kenyafilmcommission.com |
Hukumar Finafinai ta Kenya Hukuma ce dake kula da sha'anin fina-finai a ƙasar Kenya.[1]
Hukumar tace fina-finai ta Kenya Archived 2022-03-03 at the Wayback Machine tana ƙarƙashin ma’aikatar wasanni, al’adu da fasaha tun lokacin da aka kafa ta a shekarar 2005 har zuwa 2019 lokacin da ta koma ma’aikatar ICT, kirkire-kirkire da harkokin matasa.[2] Ministan ne ya nada kwamitin. Mambobin kwamitin sun hada da Chris Foot (shugaban hukumar), Judy Bisem, Njoki Muhoho, Julius Lamaon, Michael Onyango, Mwaniki Mageria da Felix Mugabe. [3]
Hukumar fina-finai ta Kenya tana tallafawa masana'antar fina-finai ta Kenya ta hanyar samar da kayan aiki don nunawa da yin fim, da kuma shirya tarurrukan ilimi daban-daban kan samarwa ga masu shirya fina-finai na gida. Hukumar ta kuma kafa wata ma’adanar bayanai da za ta jera masu shirya fina-finai, wakilai, hazikan ‘yan gida, masu ruwa da tsaki da masu samar da hidima a masana’antar fim ta Kenya. Hukumar Fina-finai ta Kenya memba ce ta Ƙungiyar hukumomin finafinai ta duniya wato Association of Film Commissions International.[4]