Bettinah Tianah | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Uganda, 10 Nuwamba, 1993 (30 shekaru) |
ƙasa | Uganda |
Karatu | |
Harsuna | Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | mai gabatarwa a talabijin, Jarumi da model (en) |
Bettinah Tianah kuma Betty Nassali, (an haife ta a ranar 10 ga watan Nuwamba 1993) ta kasance 'yar Uganda ce mai aikin telebiji da yin fim. An santa da yin shirye-shiryen telebiji na Youth Voice, Be My Date,[1] da kuma Style Project. Ta kuma fito acikin mataki babba (Rhona) acikin Hostel television series.
A sanda take shekara 15, Tianah ta fara aiki a NBS Television amatsayin mai gabatar da shirin Youth Voice. Ta kuma gudanar da shirin matchmaking na telebiji da ake kira da Be My Date[2][3] a shekarar 2015 a NTV Uganda, ta maye gurbin Anita Fabiola, da kuma gudanar da shirin fashion show maisuna The Style Project tun daga 2017. Tianah tafara shirin fim din ta na farko ne da ta fito amatsayin Rhona, wata "bad girl" a Ugandan television series The Hostel a kashi na hudun karshe.
Tianah kuma ta gudanar da bikin red carpet UNAA Convention a Washington D.C., inda ta zama yar Uganda ta farko data gudanar da shirin.[4] Tianah Kuma model ce, ta sanya hannu da Kungiyar Creative Industries a 2017. Ta yi photoshoot din ta na farko a Birnin Paris.[5]
Tianah tayi digiri a fannin Jarida da Cavendish University. Kafin nan ta fara yin digiri a fannin Human Resources Management a Makerere University Business School (MUBS), amma sai ta fasa domin komawa fannin Jarida.[6]