Betika | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | Houedji |
Haihuwa | Bouaké, |
ƙasa | Ivory Coast |
Karatu | |
Harsuna | Faransanci |
Sana'a | |
Sana'a | Jarumi da mawaƙi |
Bétika (An kuma haife ta Brigitte Houedji, Grand-Bassam, Ivory Coast) ita mawakiya ce kuma yar'fim daga Ivory Coast.[1][2][3]
An haife ta a tsahon Babban Birnin Mulkin mallakar Faransa na Grand-Bassam, dake gabashin babban birnin Abidjan, Houedji ta kasance a zagayen karshe a "Le Famesol", da aka yi a Grand-Bassam acikin shekarar 1987. Da son ta da kwarewarta a waka, ta kuma yi shirye-shirye da tafiye-tafiye da ensembles na François Lougah da Antoinette Konan a nasarance. A 1996, Bétika ta saki albam dinta n'a farko, "Ma Vie" ("My Life" acikin turanci). A 2000, ta saki album na biyu, Millenium 2000 Ah les Hommes!. A 2005 ta saki album na uku, Missié Pardon (Fakaloh). Ta hanyar wakar ta, Bétika ta yada soyayyan ma'aurata. Waken ta na maida hankali akan so da kauna ga mutane baki daya. Da sanayya, masoya wakar Ivory coast sun bata sunan "L’avocate de l’Amour" ("The Advocate of Love").[2][3][4]
A 2006, Bétika tayi nasarar samun kyautuka uku, wanda suka hada da "Georges Taï Benson" award a Ivorian Music Awards. Kuma ta zama best female artist a wurin bikin wakar ta "Fakaloh".[4]